Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka.

  2. Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka.

  3. Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.

  4. Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.

  5. Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.

  6. Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba.

  7. Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci.

  8. Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka.

  9. Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.

  10. Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.

  11. Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.

  12. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.

  13. Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.

  14. Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.

  15. Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.

  16. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.

  17. Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu.

  18. Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.

  19. Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.

  20. Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.

  21. Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka.

  22. Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.

  23. Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.

  24. Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka.

  25. Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya.