Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sai sarki ya aika a kawo Shimeyi, ya ce masa, “Ban sa ka rantse da sunan Ubangiji, na kuma ja maka kunne cewa, ‘A ranar da ka kuskura ka bar nan ka tafi wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba’? A lokacin ka ce mini, ‘Abin da ka faɗa yana da kyau. Zan kuwa kiyaye.’

  2. To, me ya sa ba ka kiyaye rantsuwar da ka yi ga Ubangiji, ka kuma yi biyayya da umarnin da na ba ka ba?”

  3. Sarki ya ce wa Shimeyi, “Ka sani a zuciyarka dukan muguntar da ka yi wa mahaifina Dawuda. Yanzu Ubangiji zai sāka maka saboda muguntarka.

  4. Amma za a yi wa Sarki Solomon albarka, sarautar Dawuda kuma za tă kasance a tsare a gaban Ubangiji har abada.”

  5. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

  6. A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba.

  7. Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai.

  8. A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

  9. “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba.

  10. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta.

  11. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

  12. Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan.

  13. Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya,

  14. zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.

  15. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna.

  16. In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”

  17. Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.

  18. Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.

  19. Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku.

  20. “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

  21. Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa.

  22. Ina niyya in gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, yadda Ubangiji ya faɗa wa mahaifina Dawuda, sa’ad da ya ce, ‘Ɗanka wanda zai gāje ka, shi zai gina haikali domin Sunana.’

  23. Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”

  24. Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya.

  25. A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.