Tsallake zuwa abun ciki

Esther

46 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Hadassah

Ayoyin da suka ambaci Esther

  1. Esta ta amsa ta ce, “Bukatata da kuma roƙona shi ne,

  2. Haman ya ƙara da cewa, “Ba duka ke nan ba, kai, ni ne kaɗai mutumin da Sarauniya Esta ta gayyata yă tafi tare da sarki zuwa liyafar da ta shirya. Ta sāke gayyace ni tare da sarki gobe.

  3. Suna cikin magana da shi ke nan, sai ga bābānnin sarki, suka iso suka kuma hanzarta da Haman zuwa liyafar da Esta ta shirya.

  4. Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta.

  5. Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.”

  6. Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata.

  7. Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?”

  8. Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.” Sai Haman ya tsorota a gaban sarki da sarauniya.

  9. Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.

  10. Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman.

  11. A wannan rana, Sarki Zerzes ya ba wa Esta mallakar Haman, abokin gāban Yahudawa. Mordekai kuma ya zo gaban sarki, gama Esta ta faɗa yadda ta haɗa dangi da shi.

  12. Sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓo daga Haman ya ba Mordekai. Esta kuma ta naɗa shi a kan mallakar Haman.

  13. Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa.

  14. Sai sarki ya miƙa wa Esta sandan sarauta na zinariya, ta kuwa tashi ta tsaya a gabansa.

  15. Sarki Zerzes ya amsa wa Esta da Mordekai mutumin Yahuda, “Domin Haman ya kai wa Yahudawa hari, na ba da mallakarsa ga Esta, an kuma rataye shi a wurin rataye mai laifi.

  16. Sarki ya ce wa Sarauniya Esta, “Yahudawa sun karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar, da kuma ’ya’ya maza goma na Haman a mazaunin masarauta a Shusha. Me suka yi a sauran lardunan sarki? Yanzu kuma mene ne roƙonki? Za a ba ki. Mece ce bukatarki? Za a biya miki.”

  17. Esta ta ce, “In sarki ya yarda, yă ba wa Yahudawa da suke Shusha izini su aikata dokan nan gobe kuma, bari kuma a rataye ’ya’ya maza goma na Haman a kan gumagumai.”

  18. Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da ’ya’yansa maza a kan gumagumai.

  19. Saboda haka Sarauniya Esta, ’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim.

  20. don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki.

  21. Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.