Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Or Lots, the Feast of Purim

19 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar.

  2. Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba.

  3. In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”

  4. Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa.

  5. Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.”

  6. Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.

  7. Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu.

  8. Za a ba da kofin rubutun a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da mutanen kowace al’umma, domin su zauna da shiri don wannan rana.

  9. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan-kada-tă-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a mazaunin masarauta da yake a Shusha. Sai Sarki da Haman suka zauna don su sha, amma birnin Shusha ya ruɗe.

  10. Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki.

  11. Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki.

  12. Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna.

  13. Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban dukan Yahudawa, ya ƙulla maƙarƙashiya game da Yahudawa, domin a hallaka su, ya kuma jefa fur (wato, ƙuri’a) don yă hallaka su.

  14. Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da ’ya’yansa maza a kan gumagumai.

  15. (Saboda haka, aka kira ranakun nan Furim, daga kalma fur). Saboda dukan abin da aka rubuta cikin wannan wasiƙa da kuma abin da suka gani, da abin da ya same su.

  16. Saboda haka Sarauniya Esta, ’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim.

  17. Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci,

  18. don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki.

  19. Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.