Tsallake zuwa abun ciki

Hammedatha

5 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Hammedatha

  1. Bayan waɗannan al’amura, sai Sarki Zerzes ya girmama Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya ɗaukaka shi, ya kuma ba shi matsayi mafi girma fiye da na dukan sauran hakiman.

  2. Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa.

  3. Ta ce, “In sarki ya yarda, in kuma na sami tagomashi daga gare shi, idan kuma ya gamshe shi yă yi abin da yake daidai, idan yana jin daɗina, bari a rubuta umarni a soke hukuncin saƙonin da Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya shirya ya kuma rubuta domin a hallaka Yahudawa a dukan lardunan sarki.

  4. ’ya’ya maza goma na Haman ɗan Hammedata, abokin gāban Yahudawa. Amma ba su taɓa dukiyarsu ba.

  5. Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban dukan Yahudawa, ya ƙulla maƙarƙashiya game da Yahudawa, domin a hallaka su, ya kuma jefa fur (wato, ƙuri’a) don yă hallaka su.