- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Purim
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sai Mordekai ya rubuta waɗannan abubuwa, ya kuma aika wasiƙu ga dukan Yahudawa ko’ina a lardunan Sarki Zerzes, na kusa da na nesa.
Ya sa su yi bikin kowace shekara a ranaku goma sha huɗu da goma sha biyar na watan Adar
a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.
Ta haka, Yahudawa suka yarda su ci gaba da bikin da suka fara, suna aikata abin da Mordekai ya rubuta musu.
Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban dukan Yahudawa, ya ƙulla maƙarƙashiya game da Yahudawa, domin a hallaka su, ya kuma jefa fur (wato, ƙuri’a) don yă hallaka su.
Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da ’ya’yansa maza a kan gumagumai.
(Saboda haka, aka kira ranakun nan Furim, daga kalma fur). Saboda dukan abin da aka rubuta cikin wannan wasiƙa da kuma abin da suka gani, da abin da ya same su.
Yahudawa suka ɗauki nawayar kafa al’adar cewa su, da zuriyarsu, da dukan waɗanda suka haɗa hannun da su, za su kiyaye waɗannan kwanaki biyu, kowace shekara yadda aka tsara, a kuma lokacin da aka keɓe dominsu.
Za a tuna, a kuma kiyaye waɗannan kwanaki a kowane zamani, cikin kowane iyali, da kuma cikin kowane lardi, da kowace birni. Kuma kada Yahudawa su fasa yin bikin waɗannan kwanakin Furim, ko su bar jikokinsu su manta da kiyaye waɗannan ranaku biyu.
Saboda haka Sarauniya Esta, ’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim.
Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci,
don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki.
Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.