Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Whirlwind

21 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da lokaci ya yi da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa sama cikin guguwa, Iliya da Elisha kuwa suna kan hanyarsu daga Gilgal.

  2. Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa.

  3. Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.

  4. Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,

  5. Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,

  6. Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.

  7. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  8. Kibiyoyinsu masu tsini ne, an ɗaura dukan bakkunansu; kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.

  9. Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa, sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa, aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai, kamar tattake kuma a cikin guguwa.

  10. Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku. Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu, mai hari ya zo daga hamada, daga ƙasar mai banrazana.

  11. Ba da jimawa ba bayan an shuka su, ba da jimawa ba bayan an dasa su, ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa, sai yă hura musu iska su yanƙwane, guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi.

  12. Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su, guguwa kuma za tă warwatsa su. Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  13. Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta, kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa; zai sauko da fushinsa da zafi, tsawatawarsa kuma da harsunan wuta.

  14. Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku!

  15. Ga shi, hadarin Ubangiji zai taso cikin hasala guguwa tana kaɗawa a kan kawunan mugaye.

  16. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.”

  17. Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye.

  18. Na duba, sai na ga guguwa ta taso daga arewa babban hadari cike da walƙiya kewaye da haske mai haske sosai. Tsakiyar wutar ta yi kamar ƙarfe mai cin wuta balbal,

  19. “Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci.

  20. Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa.

  21. Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu; kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya. Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho; zai taho ta cikin guguwa daga kudu,