Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Treasure-Houses

55 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit.

  2. Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.

  3. Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji.

  4. Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.

  5. Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai lura da ɗakunan ajiya a yankuna, cikin garuruwa, ƙauyuka da kuma hasumiyoyin tsaro.

  6. Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara.

  7. Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe.

  8. Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa.

  9. Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki.

  10. Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa.

  11. Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda.

  12. Yanzu in sarki yana so, bari a duba cikin littattafan tarihi na sarakuna na Babilon a gani ko lalle sarki Sairus ya ba da umarni a sāke gina gidan Allah a Urushalima. Bari sarki yă aiko mana da abin da ya gani game da wannan abu.

  13. Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon.

  14. Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin.

  15. Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci,

  16. Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali.

  17. Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.”

  18. A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa.

  19. ya kuma tanada masa babban ɗakin da dā ake ajiyar hadayun hatsi da turare da kayayyaki haikali, da kuma zakan hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai da aka umarta don Lawiyawa, mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi, da kuma sadakoki domin firistoci.

  20. Na umarta a tsarkake ɗakunan, sa’an nan na mayar da kayan gidan Allah a cikin ɗakunan, tare da hadayun hatsi da kuma turare.

  21. Dukan Yahuda suka kawo zakan hatsi, sabon ruwan inabi da mai cikin ɗakunan ajiya.

  22. Na sa Shelemiya firist, Zadok marubuci, da wani Balawe mai suna Fedahiya su lura da ɗakunan ajiya na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, ɗan Mattaniya ya zama mataimakinsu, domin an ɗauka waɗannan mutane amintattu ne. Aka ba su hakkin raban kayayyaki wa ’yan’uwansu.

  23. In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”

  24. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa.

  25. Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.