Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Treasure-Houses: Solomon's temple used for

22 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da Solomon's temple used for

  1. Sa’ad da aka gama aikin da Sarki Solomon sa a yi domin haikalin Ubangiji, sai ya kawo kayayyakin da mahaifinsa Dawuda ya keɓe, azurfa da zinariya da kayayyaki, ya sa su a ma’ajin haikalin Ubangiji.

  2. Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali.

  3. Bari kowane firist yă karɓi kuɗi daga masu ajiya, sa’an nan a yi amfani da su a gyara duk wani abin da ya lalace a haikali.”

  4. Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba.

  5. Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.”

  6. Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba.

  7. Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin.

  8. Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna.

  9. Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina,

  10. masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin.

  11. Ba a yi amfani da kuɗin da aka kawo a haikali don yin manyan kwanonin azurfa, lagwani, abin yayyafa ruwa, kakaki ko wani abu na zinariya, ko na azurfa domin haikalin Ubangiji ba;

  12. an ba ma’aikatan da suka gyara haikalin ne.

  13. Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.

  14. “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.

  15. Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,

  16. Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara.

  17. Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe.

  18. Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.”

  19. Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa.

  20. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan.

  21. Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin.

  22. Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.