Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribes of Israel

241 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. daga Shemida, kabilar Shemadawa; daga Hefer, kabilar Heferawa.

  2. (Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)

  3. Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700.

  4. Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu, daga Shutela, kabilar Shutelawa; daga Beker, kabilar Bekerawa; daga Tahan, kabilar Tahanawa.

  5. Waɗannan su ne kabilan Shutelawa, daga Eran, kabilar Eranawa.

  6. Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500. Waɗannan su ne kabilan Yusuf ta wurin kabilansu.

  7. Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu, daga Bela, kabilar Belawa; daga Ashbel, kabilar Ashbelawa; daga Ahiram, kabilar Ahiramawa;

  8. daga Shufam, kabilar Shufamawa; daga Hufam, kabilar Hufamawa.

  9. Zuriyar Bela daga Ard da Na’aman, daga Ard, kabilar Ardawa; daga Na’aman, kabilar Na’amawa;

  10. Waɗannan su ne kabilan Benyamin, jimillarsu ta kai 45,600.

  11. Waɗannan su ne kabilan Dan bisa ga kabilarsu, daga Shuham, kabilar Shuhamawa. Waɗannan su ne kabilan Dan.

  12. Dukansu kabilan Shuhamawa ne, jimillarsu ta kai 64,400.

  13. Zuriyar Asher bisa ga kabilansu, daga Imna, kabilar Imnawa daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa; daga Beriya, kabilar Beriyawa;

  14. daga zuriyar Beriya kuwa, daga Heber, kabilar Heberawa; daga Malkiyel, kabilar Malkiyelawa.

  15. (Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.)

  16. Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.

  17. Zuriyar Naftali bisa ga kabilansu, daga Yazeyel, kabilar Yazeyelawa; daga Guni, kabilar Guniyawa;

  18. daga Yezer, kabilar Yezerawa; daga Shillem, kabilar Shillemawa.

  19. Waɗannan su ne kabilan Naftali, jimillarsu ta kai 45,400.

  20. Dukan jimillar mazan Isra’ila ta kai 601,730.

  21. Ku aiki maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.

  22. Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?

  23. Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?

  24. Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar.

  25. Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.