Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribes of Israel

241 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Waɗannan su ne kabilan Ruben; jimillarsu ta kai 43,730.

  2. Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab,

  3. ’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji.

  4. Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa.

  5. Amma fa, zuriyar Kora ba tă mutu ba.

  6. Zuriyar Simeyon bisa ga kabilansu, daga Nemuwel, kabilar Nemuwelawa; daga Yamin, kabilar Yaminawa; daga Yakin, kabilar Yakinawa;

  7. daga Zera, kabilar Zerawa; daga Sha’ul, kabilar Sha’ul.

  8. Waɗannan su ne kabilan Simeyon; jimillarsu ta kai 22,200.

  9. Zuriyar Gad bisa ga kabilansu, daga Zafon, kabilar Zafonawa; daga Haggi, kabilar Haggiwa; daga Shuni, kabilar Shunawa;

  10. daga Ozni, kabilar Ozniyawa daga Eri, kabilar Eriyawa;

  11. daga Arod, kabilar Arodiyawa; daga Areli, kabilar Areliyawa.

  12. Waɗannan su ne kabilan Gad, jimillarsu ta kai 40,500.

  13. Er da Onan, ’ya’yan Yahuda ne, amma sun mutu a Kan’ana.

  14. Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu, daga Shela, kabilar Shelayawa daga Ferez, kabilar Ferezawa; daga Zera, kabilar Zerawa;

  15. Zuriyar Ferez kuwa, daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Hamul; kabilar Hamulawa.

  16. Waɗannan su ne kabilan Yahuda; jimillarsu ta kai 76,500.

  17. Zuriyar Issakar bisa ga kabilansu, daga Tola, kabilar Tolatawa; daga Fuwa, kabilar Fuwayawa;

  18. daga Yashub, kabilar Yashubawa; daga Shimron, kabilar Shimronawa.

  19. Waɗannan su ne kabilan Issakar; jimillarsu ta kai 64,300.

  20. Zuriyar Zebulun bisa ga kabilansu, daga Sered, kabilar Seredawa; daga Elon kabilar Elonawa; daga Yaleyel; kabilar Yaleyewa.

  21. Waɗannan su ne kabilan Zebulun, jimillarsu ta kai 60,500.

  22. Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.

  23. Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.

  24. Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;

  25. daga Asriyel, kabilar Asriyelawa; daga Shekem, kabilar Shekem;