Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Plague or Pestilence

44 ayoyi · 22 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.

  2. Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi.

  3. Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.

  4. Ubangiji kuwa ya bugi mutanen da annoba, saboda abin da suka yi da ɗan maraƙin da Haruna ya yi.

  5. zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai.

  6. Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba.

  7. Amma da suna cikin cin naman, tun ba su ma haɗiye ba, sai Ubangiji ya husata sosai a kan jama’ar, ya buge su da annoba mai zafi.

  8. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”

  9. Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu.

  10. Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.

  11. Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora.

  12. Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare.

  13. gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da ’yar’uwarsu Kozbi ’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”

  14. Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za tă manne muku, tă cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.

  15. Saboda haka Ubangiji ya aika da annoba a kan Isra’ila tun daga safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade, mutum dubu saba’in kuwa daga Dan zuwa Beyersheba suka mutu.

  16. Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus.

  17. “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, ko kuwa abokan gāba sun yi musu kwanto, a wani daga cikin biranensu, duk wata cuta, ko ciwon da ya zo,

  18. in suka yi addu’a ko roƙo ta wurin wani daga cikin mutanenka Isra’ila, kowa ya san wahalar zuciyarsa, ya kuma buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali,

  19. ‘In masifa ta zo mana, ko takobin hukunci, ko annoba ko yunwa, za mu tsaya a gabanka a gaban wannan haikalin da yake ɗauke da Sunanka, mu kuma yi kuka gare ka cikin azaba, za ka kuwa ji mu, ka cece mu.’

  20. Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,

  21. Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.

  22. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,

  23. ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.

  24. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.

  25. suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.