Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Law of Moses

65 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka.

  2. Ya koyar da farillanka ga Yaƙub, dokarka kuma ga Isra’ila. Ya miƙa turare a gabanka da kuma hadaya ta ƙonawa ɗungum a kan bagadenka.

  3. Da sarki ya ji kalmomin Doka, sai ya yage rigunansa.

  4. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki.

  5. Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”

  6. A rana ta biyu ga wata, shugabannin iyalai, tare da firistoci da Lawiyawa, suka taru kewaye da Ezra malamin Doka don su mai da hankali ga kalmomin Dokar.

  7. Suka tarar a rubuce a cikin Doka wadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa, cewa Isra’ilawa su zauna a bukkoki a lokaci bikin watan bakwai

  8. kuma cewa ya kamata su yi shelar wannan magana, su kuma yaɗa ta a duk garuruwansu da kuma cikin Urushalima cewa, “Ku fita zuwa cikin ƙasar tudu ku kawo rassa daga itatuwan zaitun da na zaitun jeji, da kuma daga dargaza, da dabino da itatuwa masu ganye, don yin bukkoki”, kamar yadda yake a rubuce.

  9. Sai mutanen suka fita suka dawo da rassa suka kuma yi wa kansu bukkoki a bisa rufin ɗakunansu, a cikin filaye, a shirayin gidan Allah, da ciki dandalin da yake kusa da Ƙofar Ruwa, da kuma a dandalin da yake a Ƙofar Efraim.

  10. Dukan jama’ar da suka komo daga zaman bauta suka yi bukkoki suka kuma zauna a cikinsu. Daga kwanakin Yoshuwa ɗan Nun har yă zuwa yau, Isra’ilawa ba su taɓa yin bikinsa haka ba. Mutane suka cika da farin ciki sosai.

  11. Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida.

  12. Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”

  13. Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa.

  14. Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.

  15. Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”

  16. amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.

  17. Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”

  18. Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”

  19. Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.

  20. An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.

  21. Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,

  22. wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.

  23. A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.

  24. Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.

  25. Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani.