Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Law of Moses: Darkness, &c at giving of, illustrative of obscurity of Mosaic age

7 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Darkness, &c at giving of, illustrative of obscurity of Mosaic age

  1. Ba ku zo ga Dutsen Sinai wanda ana iya taɓawa ba, ko ga wuta mai ci sosai, ko ga duhu baƙi ƙirin, ko

  2. ko busar ƙaho, ko ga irin wata murya mai magana da kalmomin da masu jinta suka yi roƙo kada su ƙara ji,

  3. domin ba su iya jimrewa da abin da aka umarta cewa, “Ko da ma dabba ce ta taɓa dutsen, dole a jajjefe ta da duwatsu.”

  4. Ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake, har Musa ya ce, “Ina rawar jiki don tsoro.”

  5. Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki,

  6. kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku.

  7. Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.