Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Heathen

35 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

  2. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.

  3. Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

  4. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.

  5. Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.

  6. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.

  7. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.

  8. A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.

  9. Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima.

  10. Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.

  11. “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo, ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.

  12. Duba, duhu ya rufe duniya duhu mai kauri kuma yana bisa mutane, amma Ubangiji ya taso a kanki ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.

  13. Al’ummai za su zo wurin haskenki, sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

  14. “Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke. Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki; ’ya’yanki maza daga nesa, ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.

  15. Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki; za a kawo miki wadata daga tekuna, za a kawo miki arzikin al’ummai.

  16. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji.

  17. Dukan garkunan Kedar za su taru a wurinki ragunan Nebayiwot za su yi miki hidima; za a karɓe su kamar hadayu a kan bagadenki, zan kuma darjanta haikalina mai ɗaukaka.

  18. “Su wane ne waɗannan da suke firiya kamar gizagizai, kamar kurciyoyi suna zuwa sheƙarsu?

  19. Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare, ku tattaru a can. Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!

  20. “Bari a tā da dukan al’ummai; bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat gama a can zan zauna in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.

  21. Ku fito da lauje, gama girbi ya nuna. Ku zo, ku tattaka inabin, gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba, muguntarsu da girma take!”

  22. “Ka dubi al’ummai, ka gani, ka sha mamaki. Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka, wanda ko ma an faɗa maka ba za ka gaskata ba.

  23. Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.

  24. Suna da bantsoro da firgitarwa; dokoki da ƙa’idodinsu ne kawai suka sani.

  25. Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;