Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strategy in War

63 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da Isra’ilawa suka gama kashe duk mutanen Ai a filaye da kuma a cikin jeji inda suka fafare su, kuma da aka karkashe kowane mutumin Ai da takobi sai dukan Isra’ilawa suka koma Ai suka karkashe duk waɗanda suke cikinsa.

  2. A ranan nan, dukan mutanen Ai da aka kashe, mutum dubu goma sha biyu ne maza da mata.

  3. Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.

  4. Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi.

  5. Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ”

  6. Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.

  7. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”

  8. Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.

  9. Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.

  10. Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa.

  11. Sa’an nan Isra’ila ta yi kwanto kewaya da Gibeya.

  12. Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā.

  13. Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya.

  14. Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.”

  15. Dukan mutanen Isra’ila suka taso daga wurarensu suka ja dāgā a Ba’al-Tamar, Isra’ilawan da suka yi kwanto a yammancin Geba kuwa suka fito.

  16. Sa’an nan jarumai Isra’ila dubu goma suka yi gaba suka kai wa Gibeya hari. Yaƙi kuwa ya yi zafi har mutane Benyamin ba su san masifa tana dab da su ba.

  17. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Benyamin a gaban Isra’ila; a ranar kuwa Isra’ilawa sun kashe mutum 25,100 na mutanen Benyamin, dukansu ɗauke da takuba.

  18. Sa’an nan Benyamin suka ga an ci su. To, mutanen Isra’ila sun yi ta ja da baya daga mutanen Benyamin domin suna dogara ga waɗanda sa su yi kwanto kusa da Gibeya ne.

  19. Mutanen da suke kwanto suka yi wuf suka ruga cikin Gibeya, suka bazu suka kuma karkashe dukan waɗanda suke a birnin.

  20. Mutanen Isra’ila sun riga sun shirya da ’yan kwanton cewa su murtuke hayaƙi daga birnin,

  21. a sa’an nan ne mutanen Isra’ila za su juya su fāɗa wa mutane Benyamin da yaƙi. Mutanen Benyamin sun fara karkashe mutum talatin na Isra’ila, sai suka ce, “Muna cin nasara a kansu kamar dā.”

  22. Amma da alamar hayaƙi ya fara murtukewa daga birnin, sai mutanen Benyamin suka juya suka ga hayaƙi yana murtukewa ko’ina a cikin birnin zuwa sararin sama.

  23. Sa’an nan mutanen Isra’ila suka juyo musu, mutanen Benyamin kuwa suka tsorata domin sun gane masifa ta zo musu.

  24. Saboda haka suka tsere a gaban Isra’ila zuwa wajen hamada, amma ba su iya tsere wa yaƙin ba. Mutanen Isra’ila da suka fito daga cikin birnin suka karkashe su a can.

  25. Suka kewaye mutanen Benyamin, suka kore su, suka fatattake su a wajajen Gibeya a gabashi.