Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rulers

255 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.

  2. Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.

  3. Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.

  4. Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.

  5. Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.

  6. Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.

  7. A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.

  8. Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.

  9. Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.

  10. Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.

  11. Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.

  12. Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.

  13. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.

  14. Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.

  15. Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.

  16. Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona.

  17. Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.

  18. “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

  19. Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

  20. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

  21. Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?

  22. Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.

  23. Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

  24. sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,

  25. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.