Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Polygamy

26 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In ya auri wata mace, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba.

  2. “ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.

  3. Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.

  4. In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna,

  5. to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin.

  6. Dole yă yarda cewa ɗan matar da ba ya ƙaunar ne ɗan fari, ta wurin ba shi rabo kashi biyu na dukan abin da yake da shi, gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.

  7. Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya.

  8. Na ba ka gidan maigidanka, da matan maigidanka duka. Na ba ka gidan Isra’ila da Yahuda. Da a ce dukan waɗannan sun kāsa maka, ai, da na ƙara maka.

  9. Yehohiyada ya zaɓi mata biyu dominsa, yana kuma da ’ya’ya maza da ’ya’ya mata.

  10. A wannan rana mata guda bakwai za su cafke namiji guda su ce, “Ma ciyar da kanmu mu kuma yi wa kanmu sutura; ka dai bari mu ce kai ne mijinmu. Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.”

  11. Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”

  12. Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir.

  13. Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.

  14. Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

  15. Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’

  16. ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?

  17. Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”

  18. Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”

  19. Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”

  20. Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.

  21. Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’

  22. ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,

  23. su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.

  24. To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa,

  25. Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da ’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau.