Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Old Age

39 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.

  2. ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?

  3. Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,”

  4. kafin rana da haske wata da taurari su daina haske, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;

  5. sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki, majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi, sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa, idanun da suke duba ta taga suka duhunta;

  6. sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna ƙarar niƙa kuma ya tsagaita; sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane, ba a kuwa jin waƙoƙinsu,

  7. sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi.

  8. Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe; kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula, ko guga ta tsinke a rijiya,

  9. turɓaya ta koma ƙasar da ta fito, rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.

  10. Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.

  11. ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.

  12. Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

  13. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.

  14. duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.