Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da King

74 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai kuka ce, “Bari mu naɗa sarki a kanmu kamar sauran al’umman da suke kewaye da mu,”

  2. ku tabbata kun naɗa sarki a kanku wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa ne. Dole yă zama daga cikin ’yan’uwanku. Kada ku sa baƙo a kanku, wanda ba mutumin Isra’ila ɗan’uwanku ba.

  3. Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.”

  4. Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.

  5. Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa.

  6. Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali

  7. don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.

  8. “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.”

  9. Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.”

  10. Sama’ila ya ce wa dukan mutane, “Kun ga wanda Ubangiji ya zaɓa ko? Ba wani kamar sa a cikin dukan mutane.” Sai mutane suka tā da murya suka ce, “Ran sarki yă daɗe.”

  11. Sama’ila kuwa ya bayyana wa mutane ƙa’idodin sarauta. Ya rubuta su cikin littafi ya ajiye a gaban Ubangiji. Sa’an nan ya sallame mutane, kowa ya koma gidansa.

  12. To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.”

  13. Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai.

  14. A ƙarshen shekara bakwai ɗin sai ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, ta kuma tafi wajen sarki ta roƙa a mayar mata da gidanta da filinta.

  15. Sarki kuwa yana magana da Gehazi bawan mutumin Allah, ya ce masa, “Ba ni labarin dukan abubuwan banmamakin da Elisha ya yi.”

  16. A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.”

  17. Sarki ya tambayi macen game da al’amarin, ita kuwa ta faɗa masa. Sa’an nan ya sa wani hafsa yă dubi damuwarta ya kuma ce masa, “Ka mayar mata kome da yake nata, haɗe da dukan kuɗin da aka samo daga filin, daga ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.”

  18. Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon. “Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.”

  19. Hiram ya ƙara da cewa, “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa! Ya ba Sarki Dawuda ɗa mai hikima, cike da wayo da kuma sani, wanda zai gina haikali domin Ubangiji da kuma fada wa kansa.

  20. Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai.

  21. Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima.

  22. Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.

  23. Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.

  24. Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.

  25. Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.