Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Continence

23 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’

  2. Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.

  3. To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure.

  4. Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

  5. Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.

  6. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma.

  7. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

  8. Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba.

  9. Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.

  10. To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake.

  11. Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.

  12. To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji.

  13. Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke.

  14. In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure.

  15. Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.

  16. ’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;

  17. In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.

  18. Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace.

  19. Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.

  20. Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka,

  21. tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.

  22. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.

  23. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.