Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Consolation Under Affliction: To the tempted

7 ayoyi · 22 fannoni

Ayoyi game da To the tempted

  1. Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.

  2. Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

  3. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  4. Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.

  5. Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.

  6. in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a.

  7. Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.