Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Consolation Under Affliction: To those who mourn for sin

8 ayoyi · 22 fannoni

Ayoyi game da To those who mourn for sin

  1. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

  2. Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.

  3. Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena, in ji Allahnku.

  4. Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima, ku kuma furta mata cewa aiki mai zafinta ya isa, cewa an fanshi zunubinta, cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji ninki biyu saboda dukan zunubanta.

  5. Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu

  6. Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai.

  7. Za ka sāke jin tausayinmu; za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.

  8. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.