Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Civil Service

100 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’

  2. Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba.

  3. Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba.

  4. Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka.

  5. In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.”

  6. Yayinda take cikin magana tare da sarki, sai annabi Natan ya iso.

  7. Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  8. Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka?

  9. Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’

  10. Amma bai gayyace ni bawanka, da Zadok firist, da Benahiya ɗan Yehohiyada, da kuma bawanka Solomon ba.

  11. Ranka yă daɗe, sarki, ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fadawanka, cewa ga wanda zai gāje Ranka yă daɗe, sarki ba?”

  12. Sai Dawuda ya ce, “Kira Batsheba tă shiga.” Sai ta zo gaban sarki ta kuma tsaya a gabansa.

  13. Sai sarki ya yi rantsuwa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya cece ni daga kowace damuwa,

  14. tabbatacce a yau zan aikata abin da na yi miki rantsuwa da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila; Solomon ɗanki zai zama sarki bayana, kuma shi zai zauna a kan kujerar sarautata a maimakona.”

  15. Sai Batsheba ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta kuma durƙusa a gaban sarki ta ce, “Bari ran Sarkina Dawuda yă daɗe, har abada!”

  16. Sarki Dawuda ya ce, “Ku kira mini Zadok firist, annabi Natan, da Benahiya ɗan Yehohiyada.” Da suka zo gaban sarki,

  17. sai ya ce musu, “Ku ɗauki bayin sarki tare da ku, ku kuma sa ɗana Solomon a kan dokina, ku gangara da shi zuwa Gihon.

  18. A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’

  19. Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.”

  20. Benahiya ɗan Yehohiyada ya amsa wa sarki, ya ce, “Amin! Bari Ubangiji Allah na ranka yă daɗe sarkina, yă tabbatar da haka.

  21. Kamar yadda Ubangiji ya kasance da ranka yă daɗe, sarki, haka ma bari yă kasance da Solomon, yă kuma mai da kujerar sarautarsa tă fi kujerar sarautar ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, girma!”

  22. Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon.

  23. Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!”

  24. Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa.

  25. Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna.