Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Chastity: General references

44 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.

  2. Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.

  3. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,

  4. wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.

  5. Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.

  6. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.

  7. Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.

  8. Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;

  9. amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.

  10. Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.

  11. In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

  12. Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.

  13. Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

  14. Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

  15. Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani?

  16. Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.

  17. suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci.

  18. Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.

  19. Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.

  20. Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.

  21. Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka.

  22. Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;

  23. za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.

  24. “An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.

  25. Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.