Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Chastity: Preserved by wisdom
Ayoyi game da Preserved by wisdom
Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka.
Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;
za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.