Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Chastisement

54 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa.

  2. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.

  3. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.

  4. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.

  5. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.

  6. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.

  7. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.

  8. Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.

  9. Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.

  10. Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.

  11. Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.

  12. Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.

  13. Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,

  14. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

  15. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.

  16. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

  17. Ba zan tuhume su har abada ba, ba kuwa kullum zai yi fushi ba, gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana, shi numfashin mutumin da na halitta.

  18. Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa; na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi, duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa.

  19. Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi; zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi,

  20. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna.

  21. Bayan na kauce, sai na tuba; bayan na gane, sai na sunkuyar da kaina. Na ji kunya da ƙasƙanci domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’

  22. Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji.

  23. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

  24. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

  25. Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?