Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Chastisement

54 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;

  2. alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;

  3. ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.

  4. Ba ’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba,

  5. ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.

  6. Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi.

  7. Saboda haka sai ku kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, don ku sami ƙarfin da za ku shiga, ku kuma karɓi ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaka,

  8. domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su da zuriyarsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.

  9. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.

  10. Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.

  11. “Sa’ad da an ci mutanenka Isra’ila a yaƙi ta wurin abokin gāba domin sun yi maka zunubi kuma sa’ad da suka juya suka furta sunanka, suna addu’a suka kuma yin roƙe-roƙe a gabanka a wannan haikali,

  12. sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin mutanenka Isra’ila ka kuma dawo da su zuwa ƙasar da ka ba su da kuma kakanninsu.

  13. “Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su,

  14. sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.

  15. “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko wahala ko fumfuna, ko fāra ko fāra ɗango, ko sa’ad da abokan gāba sun yi musu ƙawanya a kowane daga biranensu, dukan wata masifa ko cutar da za tă zo,

  16. sa’ad da kuwa wani cikin mutanenka Isra’ila ya yi wata addu’a ko roƙo, kowa yana sane a azabarsa da kuma zafinsa, yana buɗe hannuwansa yana duban wajen wannan haikali,

  17. sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane),

  18. don su ji tsoronka su kuma yi tafiya a hanyoyinka a kowane lokacin da suke zama a ƙasar da ka ba wa kakanninsu.

  19. “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena,

  20. in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

  21. Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;

  22. kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye.

  23. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.

  24. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  25. Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.