Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adultery: General references

128 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.”

  2. Amma saboda ka yi haka ka sa abokan gāba suka rena Ubangiji, yaron da aka haifa maka zai mutu.”

  3. Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai; yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’ sai kuma yă ɓoye fuskarsa.

  4. Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.

  5. Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu; suna abokantaka da razanar duhu.

  6. “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.

  7. “Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.

  8. “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

  9. sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.

  10. Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.

  11. Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

  12. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,

  13. wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.

  14. Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.

  15. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.

  16. Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai;

  17. amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.

  18. Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.

  19. Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.

  20. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.

  21. Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,

  22. don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani,

  23. don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.

  24. A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.

  25. Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!