Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 13:14kusan 599 K.H.

    Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da ’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’ ”

  2. Irmiya 13:15kusan 599 K.H.

    Ku ji ku kuma saurara, kada ku yi girman kai, gama Ubangiji ya yi magana.

  3. Irmiya 13:16kusan 599 K.H.

    Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.

  4. Irmiya 13:17kusan 599 K.H.

    Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta.

  5. Irmiya 13:18kusan 599 K.H.

    Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa, “Ku sauko daga kursiyinku, gama rawaninku na ɗaukaka za su fāɗi daga kawunanku.”

  6. Irmiya 13:19kusan 599 K.H.

    Za a kulle biranen da suke a Negeb, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a kwashe dukan Yahuda zuwa zaman bauta, za a kwashe su tas.

  7. Irmiya 13:20kusan 599 K.H.

    Ku tā da idanunku ku ga waɗanda suke zuwa daga arewa. Ina garken da aka ba ku tumakin da kuke taƙama a kai?

  8. Irmiya 13:21kusan 599 K.H.

    Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku waɗanda ku kanku kuka koya musu a matsayi abokai na musamman? Ashe, azaba ba za tă auko muku kamar na mace mai naƙuda ba?

  9. Irmiya 13:22kusan 599 K.H.

    In kuma kuka tambaye kanku “Me ya sa wannan ya faru da mu?” Wannan kuwa saboda yawan zunubanku ne ya sa fatarinku ya yage aka kuma wahalshe jikinku.

  10. Irmiya 13:23kusan 599 K.H.

    Mutumin Habasha zai iya canja launin fatar jikinsa ko damisa ta canja dabbare dabbarenta? Ba za ku iya yin alheri ku da kuka saba da yin mugunta ba.

  11. Irmiya 13:24kusan 599 K.H.

    “Zan watsar da ku kamar yayin da iskar hamada take hurawa.

  12. Irmiya 13:25kusan 599 K.H.

    Rabonku ne wannan, sashen da na auka muku,” in ji Ubangiji “domin kun manta da ni kuka kuma dogara ga allolin ƙarya.

  13. Irmiya 13:26kusan 599 K.H.

    Zan kware fatarinku sama ya rufe fuskarku don a iya ga tsiraicinku

  14. Irmiya 13:27kusan 599 K.H.

    zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai, karuwancinku na bankunya! Na ga ayyukanku na banƙyama a kan tuddai da kuma a filaye. Kaitonki, ya Urushalima! Har yaushe za ki ci gaba da rashin tsarki?”

  15. Irmiya 14:1kusan 605 K.H.

    Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,

  16. Irmiya 14:2kusan 605 K.H.

    “Yahuda tana makoki biranenta suna fama; suna kuka saboda ƙasar, kuka kuma tana tasowa daga Urushalima.

  17. Irmiya 14:3kusan 605 K.H.

    Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.

  18. Irmiya 14:4kusan 605 K.H.

    Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu.

  19. Irmiya 14:5kusan 605 K.H.

    Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa.

  20. Irmiya 14:6kusan 605 K.H.

    Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai suna haki kamar diloli; idanunsu sun kāsa gani saboda rashin makiyaya.”

  21. Irmiya 14:7kusan 605 K.H.

    Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu, Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka. Gama jan bayanmu ya yi yawa; mun yi maka zunubi.

  22. Irmiya 14:8kusan 605 K.H.

    Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila, Mai Cetonsa a lokutan wahala, me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar, kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce?

  23. Irmiya 14:9kusan 605 K.H.

    Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato, kamar jarumi marar ƙarfin ceto? Kana a cikinmu, ya Ubangiji, da sunanka ake kiranmu; kada ka yashe mu!

  24. Irmiya 14:10kusan 605 K.H.

    Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane, “Suna son yawace-yawace ƙwarai; ba sa hana ƙafafunsu yawo. Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba; yanzu zai tuna da muguntarsu zai kuma hukunta su saboda zunubansu.”

  25. Irmiya 14:11kusan 605 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan.