circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 11:4kusan 598 K.H.
zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.
- Irmiya 11:5kusan 598 K.H.
Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”
- Irmiya 11:6kusan 598 K.H.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.
- Irmiya 11:7kusan 598 K.H.
Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.”
- Irmiya 11:8kusan 598 K.H.
Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’ ”
- Irmiya 11:9kusan 598 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Akwai maƙarƙashiya a cikin mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima.
- Irmiya 11:10kusan 598 K.H.
Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu.
- Irmiya 11:11kusan 598 K.H.
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba.
- Irmiya 11:12kusan 598 K.H.
Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku.
- Irmiya 11:13kusan 598 K.H.
Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’
- Irmiya 11:14kusan 598 K.H.
“Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu.
- Irmiya 11:15kusan 598 K.H.
“Mene ne ƙaunatacciyata take yi a haikali da yake ta yin ƙulle-ƙullen mugayen makircinta tare da mutane masu yawa? Tsarkakar nama zai iya kawar da hukuncinki? Sa’ad da kike yin muguntarki sa’an nan ki yi farin ciki.”
- Irmiya 11:16kusan 598 K.H.
Ubangiji ya kira ki itacen zaitun mai inuwa kyakkyawa mai ’ya’ya masu kyau. Amma da ƙugin babbar hadari zai cinna masa wuta, rassansa za su kakkarye.
- Irmiya 11:17kusan 598 K.H.
Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare.
- Irmiya 11:18kusan 598 K.H.
Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi.
- Irmiya 11:19kusan 598 K.H.
Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
- Irmiya 11:20kusan 598 K.H.
Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata.
- Irmiya 11:21kusan 598 K.H.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’
- Irmiya 11:22kusan 598 K.H.
saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi, ’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa.
- Irmiya 11:23kusan 598 K.H.
Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ”
Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?
Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa; sun yi girma suna ba da ’ya’ya. Kullum sunanka yana a bakinsu amma kana nesa da zuciyarsu.
Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji; kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai. Ka ja su kamar tumakin da za a yanka! Ka ware su don ranar yanka!
Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya ciyawar kowane fili ta bushe? Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne, dabbobi da tsuntsaye sun hallaka. Ban da haka ma, mutane suna cewa, “Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.”
“In ka yi tsere da mutane a ƙafa suka kuma gajiyar da kai, yaya za ka yi gasa da dawakai? In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa, ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?