Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. ’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka; sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka. Kada ka amince da su, ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.

  2. “Zan yashe gidana, in rabu da gādona; Zan ba da wadda nake ƙauna a hannuwan abokan gābanta.

  3. Gādona ya zama mini kamar zaki a kurmi. Yana mini ruri; saboda haka na ƙi shi.

  4. Ashe, gādona bai zama mini kamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin nama da sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba? Tafi ka tattaro dukan namun jeji; ka kawo su su ci.

  5. Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina su tattake gonata; za su mai da gonata mai kyau kango marar amfani.

  6. Za tă zama kango, busasshiya da kuma kango a gabana; ƙasar duka za tă zama kango domin ba wanda ya kula.

  7. A kan dukan tsaunukan nan na hamada masu hallakarwa za su zo, gama takobin Ubangiji zai ci daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan; ba wanda zai zauna lafiya.

  8. Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa; za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba. Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe saboda zafin fushin Ubangiji.”

  9. Irmiya 12:14kusan 603 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu.

  10. Irmiya 12:15kusan 603 K.H.

    Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa.

  11. Irmiya 12:16kusan 603 K.H.

    In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye’ kamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata.

  12. Irmiya 12:17kusan 603 K.H.

    Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji.

  13. Irmiya 13:1kusan 599 K.H.

    Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Tafi ka sayo abin ɗamara na lilin ka sha ɗamara da shi, amma kada ka bari yă taɓa ruwa.”

  14. Irmiya 13:2kusan 599 K.H.

    Saboda haka na sayo abin ɗamara, yadda Ubangiji ya umarce ni, na kuwa sha ɗamara da shi.

  15. Irmiya 13:3kusan 599 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo mini sau na biyu cewa,

  16. Irmiya 13:4kusan 599 K.H.

    “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi yanzu zuwa Fera ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.”

  17. Irmiya 13:5kusan 599 K.H.

    Saboda haka na tafi na ɓoye shi a Fera, yadda Ubangiji ya ce mini.

  18. Irmiya 13:6kusan 599 K.H.

    Bayan ’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.”

  19. Irmiya 13:7kusan 599 K.H.

    Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam.

  20. Irmiya 13:8kusan 599 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  21. Irmiya 13:9kusan 599 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima.

  22. Irmiya 13:10kusan 599 K.H.

    Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani!

  23. Irmiya 13:11kusan 599 K.H.

    Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’

  24. Irmiya 13:12kusan 599 K.H.

    “Faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi.’ In kuwa suka ce maka, ‘Ba mu san cewa ya kamata a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi ba?’

  25. Irmiya 13:13kusan 599 K.H.

    Sai ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan cika dukan waɗanda suke zama a ƙasar da buguwa, har ma da sarakunan da suke zama a kursiyin Dawuda, firistoci, annabawa da dukan waɗanda suke zaune a Urushalima.