Tsallake zuwa abun ciki

circa 1406–1380 BC

Conquest of Canaan

Joshua leads Israel across the Jordan into the promised land, defeating the Canaanite kingdoms one by one.

658 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Yoshuwa 6:3kusan 1451 K.H.

    Da kai da dukan sojoji, ku zaga birnin sau ɗaya kullum. Ku yi haka har kwana shida.

  2. Yoshuwa 6:4kusan 1451 K.H.

    Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni.

  3. Yoshuwa 6:5kusan 1451 K.H.

    Sa’ad da kuka ji sun ɗauki dogon lokaci suna busa ƙaho, sai mutane gaba ɗaya su tā da murya su yi ihu da ƙarfi; katangar birnin kuwa za tă rushe, sai sojoji su haura, ko wanne yă nufi inda ya fuskanta kai tsaye.”

  4. Yoshuwa 6:6kusan 1451 K.H.

    Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, “Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa.”

  5. Yoshuwa 6:7kusan 1451 K.H.

    Sai ya umarci jama’a ya ce, “Mu je zuwa! Ku zaga birnin, masu tsaro da makamai su shiga gaban akwatin alkawarin Ubangiji.”

  6. Yoshuwa 6:8kusan 1451 K.H.

    Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su.

  7. Yoshuwa 6:9kusan 1451 K.H.

    Masu tsaro da makamai kuma suna gaban firistoci waɗanda suke busa ƙahoni, masu tsaro daga baya kuma suna bin akwatin alkawari, ana ta busa ƙahoni.

  8. Yoshuwa 6:10kusan 1451 K.H.

    Amma Yoshuwa ya umarci mutane ya ce, “Kada ku yi kururuwar yaƙi, kada ku tā da murya, kada ku ce kome, sai ranar da na ce ku yi ihu, a sa’an nan ne sai ku yi ihu!”

  9. Yoshuwa 6:11kusan 1451 K.H.

    Sai ya sa aka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji aka kewaye birnin da shi sau ɗaya, sa’an nan mutane suka dawo masauƙinsu suka kwana a can.

  10. Yoshuwa 6:12kusan 1451 K.H.

    Kashegari, Yoshuwa ya tashi da sassafe, firistoci kuma suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji.

  11. Yoshuwa 6:13kusan 1451 K.H.

    Firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai suka shiga gaba, suna takawa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji suna kuma busa ƙahoni, masu tsaro ɗauke da makamai suna gabansu, sai masu tsaro da suke baya suna biye da akwatin alkawarin Ubangiji.

  12. Yoshuwa 6:14kusan 1451 K.H.

    A rana ta biyu suka sāke zaga birnin sau ɗaya, suka kuma koma masauƙinsu. Haka suka yi har kwana shida.

  13. Yoshuwa 6:15kusan 1451 K.H.

    A rana ta bakwai, suka tashi da sassafe suka zaga birnin sau bakwai yadda suka saba. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai.

  14. Yoshuwa 6:16kusan 1451 K.H.

    A zagawa ta bakwai, da firistoci suka busa ƙahoni, sai Yoshuwa ya ba sojojin umarni ya ce, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin!

  15. Yoshuwa 6:17kusan 1451 K.H.

    Birnin da dukan abin da yake cikinta za a miƙa su ga Ubangiji. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye ’yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.

  16. Yoshuwa 6:18kusan 1451 K.H.

    Amma, ba za ku ɗauki wani abin da za a hallaka ba, idan kuka yi haka, za ku jawo masifa da hallaka a kan mutanen Isra’ila a inda kuka sauka.

  17. Yoshuwa 6:19kusan 1451 K.H.

    Dukan azurfa da zinariya, da kwanonin tagulla da na ƙarfe, keɓaɓɓu ne ga Ubangiji, dole a sa su cikin ma’ajin Ubangiji.”

  18. Yoshuwa 6:20kusan 1451 K.H.

    Da aka busa ƙahoni, sojoji suka yi ihu, da jin ƙarar ƙahoni, mutane suka kuma yi ihu, sai katangar ta rushe; dukan mutanen kuwa suka shiga birnin kai tsaye, suka yi nasara a kanta.

  19. Yoshuwa 6:21kusan 1451 K.H.

    Suka miƙa wa Ubangiji birnin, suka hallaka kowane abu mai ran da yake cikin birnin da takobi, maza da mata, yara da tsofaffi, shanu, tumaki da jakuna.

  20. Yoshuwa 6:22kusan 1451 K.H.

    Yoshuwa ya ce wa mutanen nan biyu waɗanda suka je leƙen asirin ƙasar, “Ku shiga gidan karuwan nan ku fitar da ita da duk waɗanda suke nata bisa ga alkawarin da kuka yi mata.”

  21. Yoshuwa 6:23kusan 1451 K.H.

    Sai samarin waɗanda suka je leƙen asirin suka shiga suka fitar da Rahab, mahaifinta da mahaifiyarta, da ’yan’uwanta da duk abin da yake nata. Suka fitar da iyalinta gaba ɗaya suka sa su a wani wuri, ba a cikin masauƙin Isra’ilawa ba.

  22. Yoshuwa 6:24kusan 1451 K.H.

    Sa’an nan suka ƙona birnin tare da dukan abin da yake ciki tatas, amma suka sa azurfa da zinariya da kayan tagulla da na ƙarfe a cikin ma’aji na haikalin Ubangiji.

  23. Yoshuwa 6:25kusan 1451 K.H.

    Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwan nan bai kashe ta ba, ita da iyalinta da duk abin da yake nata, domin ita ta ɓoye mutanen da Yoshuwa ya aika Yeriko don su leƙo asirin ƙasar kuma ta zauna tare da Isra’ilawa har wa yau.

  24. Yoshuwa 6:26kusan 1451 K.H.

    A lokacin nan Yoshuwa ya yi wannan alkawari cewa, “Ubangiji zai tsine wa mutumin da zai yi ƙoƙarin sāke gina birnin nan, Yeriko. “A bakin ran ɗan farinsa zai kafa harsashin birnin; a bakin ran ɗan autansa kuma zai sa ƙofofin birnin.”

  25. Yoshuwa 6:27kusan 1451 K.H.

    Ubangiji ya kasance tare da Yoshuwa, aka kuma san da shi a duk fāɗin ƙasar.