Tsallake zuwa abun ciki

Zion

139 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Sion

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Zion

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon da yake kewaye da Diyar Sihiyona. Ya auna da igiyar awo bai fasa hallaka ta ba. Ya sa katanga da katanga duk suka lalace.

  2. Dattawan Diyar Sihiyona sun zauna shiru a ƙasa; suka kuma sa rigar buhu. ’Yan matan Urushalima suka sunkuyar da kawunansu ƙasa.

  3. Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke?

  4. Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.

  5. Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane!

  6. Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.

  7. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.

  8. An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.

  9. Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona; ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki. Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki, gama ranar Ubangiji tana zuwa. Tana gab da faruwa

  10. A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro.

  11. Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona, ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku, gama ya ba ku ruwan bazara cikin adalci. Yakan aika muku yayyafi a yalwace, na bazara da na kaka, kamar dā.

  12. Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.

  13. “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.

  14. Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba, zan gafarta.”

  15. Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”

  16. Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne, ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya, waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!

  17. Ku da kuke zama a Lakish, ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi. Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, gama an sami laifofin Isra’ila a cikinku.

  18. kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta.

  19. Don haka, saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma ta zama tarin juji, tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.

  20. Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.

  21. Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”

  22. Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.

  23. Amma yanzu al’ummai da yawa suna gāba da ke. Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, bari mu zuba wa Sihiyona ido.”

  24. “Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona, gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe; zan ba ki kofatan tagulla domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.” Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya.

  25. Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima!