Tsallake zuwa abun ciki

Samaria

113 verses

32.2800, 35.1900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Samaria

Tace bisa littafi
  1. ‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?

  2. Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,

  3. ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”

  4. Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim? Sun fanshi Samariya daga hannuna?

  5. “A cikin annabawan Samariya na ga wannan abin banƙyama. Suna annabci ta wurin Ba’al suna ɓad da mutanena Isra’ila.

  6. Za ki sāke dasa gonakin inabi a kan tussan Samariya; manoma za su yi shuka a kansu su kuma ji daɗin amfaninsu.

  7. sai ga mutane tamanin daga Shekem, Shilo da Samariya suka zo da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage, suka kawo hadayun gari da turare tare da su a gidan Ubangiji.

  8. Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata.

  9. Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.

  10. “ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su,

  11. ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā.

  12. Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi ’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.

  13. Za ki cika da buguwa da baƙin ciki, kwaf lalaci da kaɗaici, kwaf na ’yar’uwarki Samariya.

  14. a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;

  15. Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka?

  16. Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya.

  17. Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.

  18. Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu, domin sun tayar wa Allahnsu. Za a kashe su da takobi; za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa, za a ɓarke matansu masu ciki.”

  19. Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”

  20. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”

  21. Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”

  22. Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne, ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya, waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!

  23. Mutane daga Negeb za su mamaye duwatsun Isuwa, mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki ƙasar Filistiyawa. Za su mamaye filayen Efraim da Samariya, Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.

  24. Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

  25. Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?