Tsallake zuwa abun ciki

Samaria

113 verses

32.2800, 35.1900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Samaria

Tace bisa littafi
  1. “Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.

  2. Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili.

  3. To, ya zama dole yă bi ta Samariya.

  4. Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf.

  5. Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?”

  6. Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.)

  7. Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”

  8. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.

  9. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.

  10. To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne,

  11. Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna.

  12. Sa’an nan ikkilisiya ko’ina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji.

  13. Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai.