Tsallake zuwa abun ciki

Jerusalem

753 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jerusalem's

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jerusalem

Tace bisa littafi
  1. sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.

  2. Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji.

  3. Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”

  4. “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’

  5. ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya sarakunan Yahuda da kuma mutanen Urushalima. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku saurara! Zan kawo masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa.

  6. “ ‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji.

  7. Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”

  8. Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.”

  9. A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”

  10. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa, “Zan sa su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwa mai dafi, domin daga annabawan Urushalima rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.”

  11. Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji.

  12. “ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar.

  13. Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima.

  14. Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau;

  15. “Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’

  16. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  17. In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.

  18. waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,

  19. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima,

  20. Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.

  21. (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.)

  22. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.

  23. Saboda haka, ku ji maganar Ubangiji, dukanku masu zaman bauta waɗanda na aika daga Urushalima zuwa Babilon.

  24. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya,

  25. Sojojin sarkin Babilon a lokacin suna ƙawanya wa Urushalima annabi Irmiya kuwa yana a tsare a sansanin matsara a fadar Yahuda.