Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya.

  2. Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi.

  3. Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.

  4. Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.

  5. Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”

  6. Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,

  7. Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

  8. Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”

  9. Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.

  10. Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’

  11. Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.

  12. Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.

  13. Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.

  14. Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,

  15. “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?” Suka amsa, “Na Kaisar.”

  16. Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

  17. Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.

  18. Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,

  19. Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,

  20. Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’

  21. Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”

  22. Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”

  23. Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.

  24. Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’

  25. Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,