Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.
Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”
Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.
Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.
Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”
Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”
Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.
Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”
Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)
Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”
Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.”
Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”
Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.
A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar
har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.
Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.
A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai.
Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”
Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa.
Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”
Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.
Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su.
Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”