Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?”

  2. babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.

  3. “Babu tsoron Allah a idanunsu.”

  4. Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.

  5. Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci.

  6. Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,

  7. gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,

  8. Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba

  9. Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma,

  10. da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin.

  11. To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.

  12. In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba.

  13. Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”

  14. Dawuda ya faɗi haka sa’ad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don yă yi ayyuka ba.

  15. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.

  16. Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah,

  17. Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,

  18. ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah.

  19. Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

  20. Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

  21. Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!

  22. Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.

  23. Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa!

  24. Sam, ko kaɗan! Mun mutu ga zunubi; ta yaya za mu ci gaba da rayuwa a cikinsa kuma?

  25. Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.