God
Ayoyin da suka ambaci God
A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can.
Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani.
Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina.
Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.
Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci.
Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.
Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ” in ji Ubangiji.
“Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona.
Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.
A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba.
A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
“Ni kaina na faɗa, “ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.
Amma kamar mace marar aminci ga mijinta, haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji.
An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.
“Ku komo, mutane marasa bangaskiya; zan warkar da ku daga ja da bayanku.” “I, za mu zo wurinka, gama kai ne Ubangiji Allahnmu.
Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai da duwatsu banza ne; tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne akwai ceton Isra’ila.
Bari mu kwanta mu sha kunya, bari kuma kunyarmu ta rufe mu. Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, da mu da kakanninmu; daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.”
“In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba,
kuma in cikin gaskiya da adalci ka rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ to al’ummai za su sami albarka ta wurinsa kuma a cikinsa za su ɗaukaka.”
Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima. “Ku nome ƙasarku kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa.
Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji ku yi wa zukatanku kaciya, ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima, in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci ba wanda zai kashe ta.
Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba.
“A wannan rana,” in ji Ubangiji, “sarki da shugabanni za su fid da zuciya, firistoci za su razana, annabawa kuma za su yi mamaki.”
Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.”