Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne.

  2. Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.

  3. Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.

  4. Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka.

  5. Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci.

  6. Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.

  7. Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka.

  8. Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai.

  9. Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka.

  10. Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka.

  11. Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka.

  12. Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka.

  13. Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne.

  14. Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka.

  15. Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina.

  16. Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.

  17. Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba.

  18. Waƙar haurawa. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.

  19. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.

  20. Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.

  21. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

  22. tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

  23. Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

  24. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;

  25. Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.