God
Ayoyin da suka ambaci God
Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”
Waƙar haurawa. Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai.
In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka.
Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.
Waƙar haurawa. Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
“Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”
Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka.
Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,
in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”
Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,
“Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci.
Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.
“A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena.