Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela

  2. Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa.

  3. Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa.

  4. Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,

  5. Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki.

  6. Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.

  7. Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā.

  8. Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai.

  9. Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.

  10. Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah.

  11. Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela

  12. gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.

  13. Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.

  14. Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata

  16. Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.

  17. Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.

  18. Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.

  19. Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.

  20. gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.

  21. Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.

  22. Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.

  23. Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.

  24. Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.

  25. Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu.