Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.

  2. Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.

  3. Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

  4. Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah?

  5. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.

  6. Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa.

  7. Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice.

  8. Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.

  9. Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.

  10. Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.

  11. Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.

  12. Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.

  13. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.

  14. Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.

  15. Zabura ta Asaf. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.

  16. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.

  17. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”

  18. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  19. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.

  20. Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.

  21. na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.

  22. Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana.

  23. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

  24. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

  25. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.