God
Ayoyin da suka ambaci God
Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.
Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.
Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,
’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo. Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.
Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”
Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.
A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka taɓa sa in sha kunya.
Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni.
Ka zama dutsena da kagarata, inda kullum zan je. Ka ba da umarni a cece ni, gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata.
Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye, da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.
Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka.
Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi.
Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini.
Suna cewa, “Allah ya yashe shi; mu fafare shi mu kama shi, gama ba wanda zai kuɓutar da shi.”
Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni.
Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau.
Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba.