Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ta Dawuda. Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.

  2. Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;

  3. gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.

  4. Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,

  5. ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.

  6. Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.

  7. Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.

  8. Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro?

  9. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  10. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.

  11. Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

  12. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.

  13. Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema.

  14. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona.

  15. Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni, Ubangiji zai karɓe ni.

  16. Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji; ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya saboda masu danne ni.

  17. Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai.

  18. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.

  19. Ta Dawuda. A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.

  20. Ka ji kukata ta neman jinƙai yayinda nake kira ka don neman taimako, yayinda nake daga hannuwana wajen Wurinka Mafi Tsarki.

  21. Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji da abin da hannuwansa suka yi ba, zai rushe su ba kuwa zai ƙara gina su ba.

  22. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai.

  23. Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

  24. Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa.

  25. Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.