Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Zabura ta Dawuda. Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

  2. Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

  3. Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.

  4. Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take.

  5. Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.

  6. Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.

  7. Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.

  8. Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”

  9. Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.

  10. Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.

  11. Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.

  12. Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.

  13. Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

  14. Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki.

  15. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.

  16. Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro.

  17. A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.

  18. “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka?

  19. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”

  20. Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

  21. don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

  22. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.

  23. Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona.

  24. Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.

  25. Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata.