Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.

  2. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

  3. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  4. Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela

  5. Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.

  6. Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela

  7. Ta Dawuda. A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina.

  8. A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.

  9. Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.

  10. Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka;

  11. ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.

  12. Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā.

  13. Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

  14. Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.

  15. Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

  16. Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.

  17. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.

  18. To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.

  19. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.

  20. Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.

  21. Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala.

  22. Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka ’yantar da ni daga wahalata.

  23. Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka.

  24. Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka.

  25. Ka fanshi Isra’ila, ya Allah, daga dukan wahalarsu!