Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,

  2. alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.

  3. Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.

  4. “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”

  5. Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

  6. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.

  7. Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

  8. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.

  9. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.

  10. Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,

  11. ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.

  12. Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.

  13. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”

  14. Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.

  15. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.

  16. Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”

  17. Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”

  18. Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.

  19. Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon

  20. don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.

  21. Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  22. Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.

  23. Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”

  24. Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.”

  25. A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa,